Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 9:30-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Sai idanunsu suka buɗe. Amma Yesu ya kwaɓe su ƙwarai, ya ce, “Kada fa kowa ya ji labarin.”

31. Amma suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk ƙasar.

32. Sun tashi ke nan, sai aka kawo masa wani bebe mai aljan.

33. Bayan an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, suka ce, “Kai! Ba a taɓa ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba.”

34. Amma sai Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”

35. Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

Karanta cikakken babi Mat 9