Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 9:16-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle, don mahon zai kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.

17. Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai salkunan su fashe, ruwan inabin ya zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. Ta haka an tserar da duka biyu ke nan.”

18. Yana cikin yi musu magana haka, sai ga wani shugaban jama'a ya zo, ya yi masa sujada, ya ce, “Yanzu yanzu 'yata ta rasu, amma ka zo ka ɗora mata hannu, za ta rayu.”

19. Sai Yesu ya tashi, ya bi shi tare da almajiransa.

20. Ga kuma wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa,

21. domin ta ce a ranta, “Ko da mayafinsa ma na taɓa, sai in warke.”

22. Sai Yesu ya juya, yă gan ta, ya ce, “'Yata, ki yi farin ciki, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take matar ta warke.

23. Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya,

24. sai ya ce, “Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.” Sai suka yi masa dariyar raini.

25. Amma da aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta tashi.

26. Wannan labarin kuwa ya bazu a duk ƙasar.

27. Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna ɗaga murya suna cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu.”

28. Da ya shiga wani gida sai makafin suka zo gare shi. Yesu ya ce musu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?” Sai suka ce masa, “I, ya Ubangiji!”

29. Sa'an nan ya taɓa idanunsu, ya ce, “Yă zama muku gwargwadon bangaskiyarku.”

Karanta cikakken babi Mat 9