Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 9:10-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sa'ad da kuwa Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa.

11. Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

12. Amma da Yesu ya ji haka ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya.

13. Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba.’ Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”

14. Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, “Don me mu da Farisiyawa mukan yi azumi, amma naka almajiran ba sa yi?”

15. Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.

16. Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle, don mahon zai kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.

17. Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai salkunan su fashe, ruwan inabin ya zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. Ta haka an tserar da duka biyu ke nan.”

18. Yana cikin yi musu magana haka, sai ga wani shugaban jama'a ya zo, ya yi masa sujada, ya ce, “Yanzu yanzu 'yata ta rasu, amma ka zo ka ɗora mata hannu, za ta rayu.”

19. Sai Yesu ya tashi, ya bi shi tare da almajiransa.

20. Ga kuma wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa,

Karanta cikakken babi Mat 9