Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 5:18-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome.

19. Don haka duk wanda ya yar da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnan nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a Mulkin Sama.

20. Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”

21. “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’

22. Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.

23. Saboda haka, in kana cikin miƙa sadakarka a kan bagadin hadaya, a nan kuma ka tuna ɗan'uwanka na da wata magana game da kai,

24. sai ka dakatar da sadakarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan'uwanka, sa'an nan ka zo ka miƙa sadakarka.

25. Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari'a, don kada mai kararka ya bashe ka ga alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga dogari, a kuma jefa ka a kurkuku.

26. Hakika ina gaya maka, ba za ka fita daga nan ba, sai ka biya duk, babu sauran ko anini.”

27. “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’

Karanta cikakken babi Mat 5