Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Wa'azi a kan Dutse

1. Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa.

2. Sai ya buɗe baki ya koya musu.

Albarku

3. “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.

4. “Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.

5. “Albarka tā tabbata ga masu tawali'u, domin za su gāji duniya.

6. “Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.

7. “Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu.

8. “Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah.

9. “Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.

10. “Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.

11. “Albarka tā tabbata gare ku sa'ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni.

12. Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.”

Gishiri da Haske

13. “Ku ne gishirin duniya. Amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar, mutane kuma su tattake.

14. “Ku ne hasken duniya. Ai, birnin da aka gina bisa tudu ba shi ɓoyuwa.

15. Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa'an nan ta ba duk mutanen gida haske.

16. To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”

Koyarwar Yesu a kan Attaura

17. “Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su.

18. Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome.

19. Don haka duk wanda ya yar da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnan nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a Mulkin Sama.

20. Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”

Koyarwar Yesu a kan Fushi

21. “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’

22. Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.

23. Saboda haka, in kana cikin miƙa sadakarka a kan bagadin hadaya, a nan kuma ka tuna ɗan'uwanka na da wata magana game da kai,

24. sai ka dakatar da sadakarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan'uwanka, sa'an nan ka zo ka miƙa sadakarka.

25. Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari'a, don kada mai kararka ya bashe ka ga alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga dogari, a kuma jefa ka a kurkuku.

26. Hakika ina gaya maka, ba za ka fita daga nan ba, sai ka biya duk, babu sauran ko anini.”

Koyarwar Yesu a kan Zina

27. “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’

28. Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha'awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita.

29. In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Gidan Wuta.

30. In kuma hannunka na dama, yana sa ka yi laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta.”

Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure

31. “An kuma ce, ‘Kowa ya saki matarsa, sai ya ba ta takardar saki.’

32. Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”

Koyarwar Yesu a kan Rantsuwa

33. “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse a kan ƙarya, sai dai ka cika wa'adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’

34. Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah,

35. ko da ƙasa, domin ita ce matashin ƙafarsa, ko kuma da Urushalima, domin ita ce birnin Babban Sarki.

36. Kada kuwa ka rantse da kanka, don ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya fari ko baƙi ba.

37. Abin da duk za ku faɗa ya tsaya a kan ‘I’ ko ‘A'a’ kawai. In dai ya zarce haka, to, daga Mugun ya fito.”

Koyarwar Yesu a kan Ramawa

38. “Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma haƙori ne.’

39. Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma.

40. In kuwa wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma.

41. In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma.

42. Kowa ya roƙe ka, ka ba shi, mai neman rance a wurinka kuwa, kada ka hana shi.”

Ƙaunar Magabta

43. “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan'uwanka, ka ƙi magabcinka.’

44. Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu'a,

45. domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.

46. In masoyanku kawai kuke ƙauna, wane lada ne da ku? Ashe, ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?

47. In kuwa 'yan'uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al'ummai ma ba haka suke yi ba?

48. Saboda haka sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama take cikakke.”