Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 4:7-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

8. Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.

9. Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.”

10. Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa,‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada,Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

11. Sa'an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala'iku sun zo suna yi masa hidima.

12. To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili.

13. Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali,

14. domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,

15. “Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali,Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun,Da kuma ƙasar Galili ta al'ummai,

16. Mazaunan duhu sun ga babban haske,Mazaunan bakin mutuwa da fargabarta,Haske ya keto musu.”

17. Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”

18. Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.

19. Sai ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”

20. Nan da nan, sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi.

21. Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su.

22. Nan take suka bar jirgin duk da ubansu, suka bi shi.

23. Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.

Karanta cikakken babi Mat 4