Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 4:3-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”

4. Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba,Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”

5. Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,

6. ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa,‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai,’da kuma‘Za su tallafe ka,Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”

7. Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

8. Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.

9. Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.”

10. Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa,‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada,Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

11. Sa'an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala'iku sun zo suna yi masa hidima.

12. To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili.

13. Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali,

14. domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,

Karanta cikakken babi Mat 4