Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 4:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan sai Ruhu ya kai Yesu cikin jeji, domin Iblis yă gwada shi.

2. Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.

3. Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”

4. Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba,Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”

5. Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,

6. ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa,‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai,’da kuma‘Za su tallafe ka,Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”

Karanta cikakken babi Mat 4