Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 3:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A wannan zamani ne Yahaya Maibaftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya,

2. yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”

3. Wannan shi ne wanda Annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce,“Muryar mai kira a jeji yana cewa,‘Ku shirya wa Ubangiji tafarki,Ku miƙe hanyoyinsa.’ ”

4. Yahaya kuwa yana saye da tufa ta gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.

5. Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk ƙasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurinsa,

6. yana yi musu baftisma a Kogin Urdun, suna bayyana zunubansu.

7. Amma da Yahaya ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa, sun taho domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?

8. Ku yi aikin da zai nuna tubarku.

9. Kada kuwa ku ɗauka a ranku cewa, Ibrahim ne ubanku, domin ina gaya muku, Allah yana da ikon ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya da duwatsun nan.

10. Koyanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyar da bata bada 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.

11. “Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.

Karanta cikakken babi Mat 3