Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 27:52-65 Littafi Mai Tsarki (HAU)

52. Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da suke barci kuma suka tashi.

53. Suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birnin, suka bayyana ga mutane da yawa.

54. Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”

55. Akwai kuma waɗansu mata da yawa a can suna hange daga nesa, waɗanda suka biyo Yesu tun daga ƙasar Galili, suna yi masa hidima.

56. A cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu da Yusufu, da kuma uwar 'ya'yan Zabadi.

57. Maraice lis sai wani mai arziki ya zo, mutumin Arimatiya, mai suna Yusufu, shi ma almajirin Yesu ne.

58. Ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya yi umarni a ba shi.

59. Yusufu ya ɗauki jikin, ya sa shi a likkafanin lilin mai tsabta,

60. ya sa shi a wani sabon kabari da ya tanadar wa kansa, wanda ya fafe a jikin dutse. Sai ya mirgina wani babban dutse a bakin kabarin, ya tafi.

61. Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun suna nan zaune a gaban kabarin.

62. Kashegari, wato, bayan ranar shiri, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka taru a gaban Bilatus,

63. suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu.

64. Saboda haka sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa'an nan su ce wa mutane wai ya tashi daga matattu. Yaudarar ƙarshe za ta fi ta farkon muni ke nan.”

65. Sai Bilatus ya ce musu, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare shi iyakar ƙoƙarinku.

Karanta cikakken babi Mat 27