Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 27:34-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha.

35. Da suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu ta jefa kuri'a.

36. Suka zauna a nan suna tsaronsa.

37. A daidai kansa aka kafa sanarwar laifinsa cewa, “Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa.”

38. Sai kuma aka gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a dama, ɗaya a hagun.

39. Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai,

40. suna cewa, “Kai da za ka rushe Haikalin, ka kuma gina shi a cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to sauko daga gicciyen mana!”

41. Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura da shugabanni suka riƙa yi masa ba'a, suna cewa,

42. “Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa. Ai, Sarkin Isra'ila ne, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mā gaskata da shi.

43. Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne.”

44. Har 'yan fashin nan da aka gicciye su tare ma, su suka zazzage shi kamar waɗancan.

45. To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.

46. Wajen ƙarfe uku kuma sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāni?” Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”

Karanta cikakken babi Mat 27