Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 27:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da gari ya waye sai duk manyan firistoci da shugabannin jama'a suka yi shawara a kan Yesu su kashe shi.

2. Sai suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga mai mulki Bilatus.

3. Sa'ad da Yahuza mai bashe shi ya ga an yanke masa hukuncin kisa, sai ya yi nadama, ya mayar wa manyan firistoci da shugabanni da kuɗi azurfa talatin ɗin nan,

4. ya ce, “Na yi zunubi da na ba da marar laifi a kashe shi.” Suka ce, “Ina ruwanmu? Kai ka jiyo!”

5. Sai ya watsar da kuɗin azurfan nan a Haikali, ya fita, ya je ya rataye kansa.

6. Amma manyan firistoci suka tsince kuɗin suka ce, “Bai halatta mu zuba su a Baitulmalin Haikali ba, don kuɗin ladan kisankai ne.”

7. Sai suka yi shawara, suka sayi filin maginin tukwane da kuɗin don makabartar baƙi.

8. Don haka, har ya zuwa yau, ana kiran filin nan filin jini.

9. Ta haka aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa, “Sun ɗauki kuɗin azurfa talatin ɗin nan, wato, awalajar shi wannan da waɗansu Isra'ilawa suka yi wa kima,

10. suka sayi filin maginin tukwane da su, yadda Ubangiji ya umurce ni.”

11. To, sai Yesu ya tsaya a gaban mai mulki, mai mulkin kuma ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa.”

12. Amma da manyan firistoci da shugabanni suka kai ƙararrakinsa, bai ce kome ba.

13. Sai Bilatus ya ce masa, “Ba ka ji yawan maganganun da suke ba da shaida a kanka ba?”

14. Amma bai ba shi wata amsa, ko da ta kalma ɗaya ba, har mai mulki ya yi mamaki ƙwarai.

Karanta cikakken babi Mat 27