Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 23:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa 'yan'uwa ne.

9. Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya ne yake gare ku, wanda yake cikin Sama.

10. Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu.

11. Amma wanda yake babba a cikinku shi zai zama baranku.

12. Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.

13. “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga. [

14. Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan matan da mazansu sun mutu, kukan yi doguwar addu'a don ɓad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.]

15. Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan kewaye ƙasashe da tekuna don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, kukan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.

16. “Kaitonku, makafin jagora, ku da kuke cewa, ‘Kowa ya rantse da Haikalin ba kome, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, sai rantsuwarsa ta kama shi.’

17. Ku makafi, wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar?

18. Kukan ce, ‘Kowa ya rantse da bagaden hadaya, ba kome. Amma duk wanda ya rantse da sadakar da aka ɗora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.’

Karanta cikakken babi Mat 23