Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 23:30-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’

31. Ta haka kuka shaidi kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa.

32. To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku!

33. Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?

34. Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami'unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba.

35. Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya.

36. Hakika, ina gaya muku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.”

37. “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!

38. Ga shi, an bar muku gidanku a yashe!

39. Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”

Karanta cikakken babi Mat 23