Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 23:18-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Kukan ce, ‘Kowa ya rantse da bagaden hadaya, ba kome. Amma duk wanda ya rantse da sadakar da aka ɗora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.’

19. Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar?

20. Don haka kowa ya rantse da bagaden hadaya, ya rantse ke nan da shi, da duk abin da yake a kansa.

21. Duk kuma wanda ya rantse da Haikalin ya rantse da shi, da kuma wanda yake zaune a cikinsa.

22. Kowa kuma ya rantse da Sama, ya rantse da kursiyin Allah, da kuma wanda yake zaune a kansa.

23. “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na'ana'a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.

24. Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!

25. “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari.

26. Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.

27. “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri.

28. Haka nan a idon mutane ku adalai ne, amma ciki sai munafunci da mugun aiki.

29. “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi gini a kan kaburburan annabawa, kuna ƙawata gubbobin adalai.

30. Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’

31. Ta haka kuka shaidi kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa.

32. To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku!

33. Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?

Karanta cikakken babi Mat 23