Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 22:15-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa.

16. Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.

17. To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?”

18. Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai!

19. Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari.

20. Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?”

21. Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa'an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”

22. Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.

23. A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya,

24. suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, ‘In mutum ya mutu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan'uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.’

25. To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan'uwansa matarsa.

Karanta cikakken babi Mat 22