Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 22:1-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yesu ya sāke yi musu magana da misalai ya ce,

2. “Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki.

3. Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa.

4. Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’

5. Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa.

6. Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su.

7. Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus.

8. Sa'an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba.

9. Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’

10. Sai bayin suka yi ta bin titi titi, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.

11. “Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba.

12. Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa.

13. Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’

14. Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”

15. Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa.

16. Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.

17. To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?”

18. Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai!

Karanta cikakken babi Mat 22