Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 21:34-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.

35. Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya.

36. Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka.

37. Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’

38. Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’

39. Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi.

40. To, sa'ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?”

41. Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”

42. Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa,‘Dutsen da magina suka ƙi,Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.Wannan aikin Ubangiji ne,A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’

43. Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.

44. Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”

45. Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane, ashe, da su yake.

46. Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama'a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne.

Karanta cikakken babi Mat 21