Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 20:17-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Yesu na tafiya Urushalima, ya ɗauki almajiran nan goma sha biyu waje ɗaya. Suna tafiya ke nan sai ya ce musu,

18. “To, ga shi, za mu Urushalima, za a kuma ba da Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa,

19. su bashe shi ga al'ummai, su yi masa ba'a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.”

20. Sa'an nan uwar 'ya'yan Zabadi ta matso wurinsa tare da 'ya'yanta, ta durƙusa a gabansa, ta roƙe shi wani abu.

21. Sai ya ce mata, “Me kike bukata?” Ta ce masa, “Ka yi umarni waɗannan 'ya'yana biyu su zauna, ɗaya a damanka, ɗaya a hagunka, a mulkinka.”

22. Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya shan ƙoƙon da ni zan sha?” Suka ce masa, “Ma iya.”

23. Sai ya ce musu, “Lalle kwa sha ƙoƙona, amma zama a damana da haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda Ubana ya riga ya shirya wa ne.”

24. Da almajiran nan goma suka ji haka, sai suka ji haushin 'yan'uwan nan biyu.

25. Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani sarakunan al'ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.

Karanta cikakken babi Mat 20