Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 17:12-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.”

13. Sa'an nan ne almajiran suka gane, ashe, zancen Yahaya Maibaftisma yake yi musu.

14. Da suka isa wurin taro, sai wani mutum ya zo gare shi, ya durƙusa a gabansa, ya ce,

15. “Ya Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, yana shan wuya ƙwarai, sau da yawa yakan faɗa wuta da kuma ruwa.

16. Na kuwa kai shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”

17. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.”

18. Sai Yesu ya tsawata masa, aljanin kuma ya rabu da shi. Nan take yaron ya warke.

19. Sa'an nan almajiran suka zo wurin Yesu a keɓe, suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fitar da shi?

20. Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku. [

21. Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a da azumi.]”

22. Tun suna ƙasar Galili, sai Yesu ya ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane,

23. za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙin ciki ya rufe su.

24. Da suka zo Kafarnahum masu karɓar rabin shekel na gudunmawar Haikali suka je wurin Bitrus, suka ce, “Malaminku yana ba da gudunmawar?”

25. Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito ko haraji, a wurin 'ya'yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?”

26. Sa'ad da kuma ya ce, “Daga wurin waɗansu,” sai Yesu ya ce masa, “Wato, 'ya'yan an ɗauke musu ke nan.

27. Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.”

Karanta cikakken babi Mat 17