Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 16:22-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawata masa, ya ce, “Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji! Wannan har abada ba zai same ka ba!”

23. Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al'amuran Allah, sai dai na mutane.”

24. Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.

25. Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.

26. Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?

27. Domin Ɗan Mutum zai zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. A sa'an nan ne zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikinsa.

28. Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin Mulkinsa.”

Karanta cikakken babi Mat 16