Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 14:26-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Sa'ad da kuwa almajiran suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka firgita suka ce, “Fatalwa ce!” Suka yi kururuwa don tsoro.

27. Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, Ni ne, kada ku ji tsoro.”

28. Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, in kai ne, to, ka umarce ni in zo gare ka a kan ruwan.”

29. Ya ce, “Zo mana.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin, ya taka ruwa ya nufi gun Yesu.

30. Amma da ya ga iska ta yi ƙarfi sai ya ji tsoro. Da ya fara nutsewa sai ya yi kururuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”

31. Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”

32. Da shigarsu jirgin iska ta kwanta.

33. Na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.”

34. Da suka haye, suka sauka a ƙasar Janisarata.

35. Da mutanen garin suka shaida shi, sai suka aika ko'ina a duk karkarar, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya,

Karanta cikakken babi Mat 14