Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 12:31-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. “Don haka ina gaya muku, ā gafarta wa mutane kowane zunubi da saɓo, amma wanda ya saɓi Ruhun, ba za a gafarta masa ba.

32. Kowa ya aibata Ɗan Mutum, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”

33. “Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, 'ya'yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, 'ya'yansa kuma munana. Don itace, da 'ya'yansa ake gane shi.

34. Ku macizai! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku mugaye ne? Don abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.

35. Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciya tasa yakan yi abin kirki, mugu kuwa, ta mummunar taskar zuciya tasa yakan yi mugun abu.

36. Ina dai gaya muku, a Ranar Shari'a duk hululun da mutum ya yi, za a bincike shi.

37. Maganarka ce za ta kuɓutar da kai, ko kuma ta hukunta ka.”

38. Waɗansu malaman Attaura da Farisiyawa suka amsa masa suka ce, “Malam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.”

39. Sai ya amsa musu ya ce, “'Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama! Amma ba wata alama da za a nuna musu sai dai ta Annabi Yunusa.

40. Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa.

41. A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su kā da su, don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.

42. A Ranar Shari'a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan, ta kā da su, don ta zo ne daga bangon duniya ta ji hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.

43. “Baƙin aljan in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa neman hutu, amma ba ya samu.

44. Sa'an nan sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’ Sa'ad da kuwa ya koma, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, ƙawatacce.

Karanta cikakken babi Mat 12