Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 10:22-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.

23. In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Ɗan Mutum zai zo.

24. “Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba ya fin ubangijinsa.

25. Ya isa wa almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba'alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?”

26. “Don haka kada ku ji tsoronsu, domin ba abin da yake a rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.

27. Abin da nake gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye.

28. Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.

29. Ashe, ba gwara biyu ne kobo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba.

30. Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake.

31. Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”

32. “Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama.

33. Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”

Karanta cikakken babi Mat 10