Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 2:12-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”

13. Yesu ya sāke fita bakin teku. Duk jama'a suka yi ta zuwa wurinsa, yana koya musu.

14. Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa a zaune yana aiki a wurin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.

15. Wata rana Yesu yana cin abinci a gidan Lawi, masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa kuma suna ci tare da shi da almajiransa, don kuwa da yawa daga cikinsu masu binsa ne;

16. to, da malaman Attaura na Farisiyawa suka ga yana cin abinci tare da masu zunubi da masu karɓar haraji, suka ce wa almajiransa, “Don me yake ci yake sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

17. Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai masu zunubi.”

18. To, almajiran Yahaya da na Farisiyawa suna azumi, sai aka zo aka ce masa, “Don me almajiran Yahaya da na Farisiyawa suke azumi, amma naka almajirai ba sa yi?”

19. Sai Yesu ya ce musu, “Ashe, abokan ango sa iya azumi tun ango na tare da su? Ai, muddin suna tare da angon, ba za su yi azumi ba.

20. Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.

21. Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle. In ma an yi, ai, sai sabon ƙyallen ya kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.

22. Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai ruwan inabin ya fasa salkunan, a kuma yi hasara tasa da ta salkunan. Sabon ruwan inabi, ai sai sababbin salkuna.”

23. Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, suna cikin tafiya sai almajiransa suka fara zagar alkamar.

Karanta cikakken babi Mar 2