Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 13:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, har su ɓad da mutane da yawa.

7. In kuma kun jin labarin yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu, kada hankalinku ya tashi. Lalle ne wannan ya auku, amma ƙarshen tukuna.

8. Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a yi ta raurawar ƙasa a wurare dabam dabam, da kuma yunwa. Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.

9. “Amma ku kula da kanku, don za su kai ku gaban majalisa, a kuma yi muku dūka a majami'u. Za a kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda sunana, domin ku ba da shaida a gabansu.

10. Amma lalle sai an fara yi wa dukan al'ummai bishara.

11. Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka miƙa ku, kada ku damu kan abin da za ku faɗa. Amma duk abin da aka yi muku baiwa da shi a lokacin nan, shi za ku faɗa, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.

12. Ɗan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu har su sa a kashe su.

13. Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe zai cetu.”

14. “Sa'ad da kuka ga an kafa mummunan aikin saɓo mai banƙyama a wurin da bai kamata ba (mai karatu fa yă fahimta), to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.

15. Wanda yake kan soro kuma kada yă sauko yă shiga gida garin ɗaukar wani abu.

16. Wanda yake gona kuma kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa.

17. Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci!

Karanta cikakken babi Mar 13