Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 13:2-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai Yesu ya ce masa, “Ka ga manyan gine-ginen nan? Ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa, da ba za a baje shi ba.”

3. Yana zaune a kan Dutsen Zaitun wanda yake kallon Haikalin sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawas suka tambaye shi a keɓe suka ce.

4. “Gaya mana yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin aukuwa?”

5. Sai Yesu ya fara ce musu, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku.

6. Mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, har su ɓad da mutane da yawa.

7. In kuma kun jin labarin yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu, kada hankalinku ya tashi. Lalle ne wannan ya auku, amma ƙarshen tukuna.

8. Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a yi ta raurawar ƙasa a wurare dabam dabam, da kuma yunwa. Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.

9. “Amma ku kula da kanku, don za su kai ku gaban majalisa, a kuma yi muku dūka a majami'u. Za a kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda sunana, domin ku ba da shaida a gabansu.

10. Amma lalle sai an fara yi wa dukan al'ummai bishara.

11. Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka miƙa ku, kada ku damu kan abin da za ku faɗa. Amma duk abin da aka yi muku baiwa da shi a lokacin nan, shi za ku faɗa, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.

12. Ɗan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu har su sa a kashe su.

13. Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe zai cetu.”

Karanta cikakken babi Mar 13