Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 11:9-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Da na gaba da na baya suka riƙa sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji!

10. Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na ubanmu Dawuda! Hosanna ga Allah!”

11. Sai ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Da dai ya dudduba kome, da yake magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyun nan.

12. Kashegari da suka tashi daga Betanya, ya ji yunwa.

13. Da ya hango wani itacen ɓaure mai ganye kore shar, sai ya je ya ga ko ya sami 'ya'ya. Da ya isa wurinsa bai ga kome ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan ɓaure ba ne.

14. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada kowa ya ƙara cin 'ya'yanka har abada!” Almajiransa kuwa suna ji.

15. Suka iso Urushalima. Ya shiga Haikalin ya fara korar masu saye da sayarwa daga ciki, ya kuma birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai,

16. ya kuma hana kowa ratsa Haikalin ɗauke da wani abu.

17. Sai ya yi musu gargaɗi ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira masujadata ɗakin addu'a na dukkan al'ummai’? Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”

18. Da manyan firistoci da malaman Attaura suka ji wannan magana suka kuma nemi hanyar hallaka shi, saboda sun tsorata da shi, don duk jama'a na mamaki da koyarwa tasa.

19. Kowace yamma kuwa Yesu yakan fita gari.

20. Suna wucewa da safe, sai suka ga ɓauren nan ya bushe har saiwarsa.

21. Bitrus kuwa ya tuna, sai ya ce masa, “Ya Shugaba, dubi! Ɓauren nan da ka la'anta ya bushe!”

22. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku gaskata da Allah.

23. Hakika, ina gaya muku, kowa ya ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku’, bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata abin da ya faɗa zai auku, sai a yi masa shi.

24. Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu'a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu.

Karanta cikakken babi Mar 11