Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 10:36-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Sai ya ce musu, “Me kuke so in yi muku?”

37. Suka ce masa, “Ka yardar mana, ranar ɗaukakarka, mu zauna ɗaya a damanka, ɗaya a hagun.”

38. Amma Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya sha da ƙoƙon da ni zan sha? Ko kwa iya a yi muku baftisma da baftismar da za a yi mini?”

39. Suka ce masa, “Ma iya.” Sai Yesu ya ce musu, “Ƙoƙon da ni zan sha, da shi za ku sha, baftismar da za a yi mini kuwa, da ita za a yi muku.

40. Amma zama a damana, ko a haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda aka riga aka shirya wa ne.”

41. Da almajiran nan goma suka ji haka, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya.

42. Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.

43. Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.

44. Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawan kowa.

45. Domin Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

46. Sai suka iso Yariko. Yana fita daga Yariko ke nan, da shi, da almajiransa, da wani ƙasaitaccen taro, sai ga wani makaho mai bara, wai shi Bartimawas, ɗan Timawas, yana zaune a gefen hanya.

47. Da ya ji dai Yesu Banazare ne, sai ya fara ɗaga murya yana cewa, “Ya Yesu, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

48. Waɗansu da yawa suka kwaɓe shi, cewa ya yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

49. Sai Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kirawo shi.” Sai suka kirawo makahon suka ce masa, “Albishirinka! Taso, yana kiranka.”

50. Sai ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu.

51. Yesu ya ce masa, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce masa, “Malam, in sami gani!”

52. Sai Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan take ya gani, ya bi Yesu, suka tafi.

Karanta cikakken babi Mar 10