Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 8:40-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. To, da Yesu ya komo, taron suka yi masa maraba domin ko a dā ma duk suna jiransa ne.

41. Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, wani shugaban majami'a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya roƙe shi ya je gidansa.

42. Yana da 'ya ɗaya tilo, mai shekara misalin goma sha biyu, tana kuma bakin mutuwa.Yana tafiya, taro masu yawa na matsa tasa,

43. sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta kuma ɓad da duk abin hannunta wajen masu magani, ba wanda ya iya warkar da ita.

44. Ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa. Nan take zubar jininta ta tsaya.

45. Sai Yesu ya ce, “Wa ya taɓa ni?” Da kowa ya yi mūsū, Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka ce, “Maigida, ai, taro masu yawa ne suke tutturarka, suna matsarka.”

46. Amma Yesu ya ce, “An dai taɓa ni, domin na ji iko ya fita daga gare ni.”

47. Da matar ta ga ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta bayyana a gaban duk jama'a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take.

48. Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”

49. Yana cikin magana, sai ga wani ya zo daga gidan shugaban majami'ar, ya ce, “Ai, 'yarka ta rasu. Kada ka ƙara wahalar da Malamin.”

50. Amma da Yesu ya ji haka, ya amsa ya ce wa shugaban majami'ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.”

Karanta cikakken babi Luk 8