Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 7:43-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. Saminu ya amsa masa ya ce, “A ganina, wanda ya yafe wa mai yawa.” Sai ya ce masa “Ka faɗa daidai.”

44. Da ya waiwaya wajen matar, ya ce wa Saminu. “Ka ga matan nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta.

45. Kai ba ka sumbance ni ba, ita kuwa, tun shigowata nan ba ta daina sumbantar ƙafafuna ba.

46. Ba ka shafa mini mai a ka ba, amma ita ta shafa man ƙanshi a ƙafafuna.

47. Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawan nan duk an gafarta mata, domin ta yi ƙauna mai yawa. Wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, ƙauna kaɗan yake yi.”

48. Sai ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”

49. Masu ci tare da shi kuwa suka fara ce wa juna, “Wannan kuwa wane ne wanda har yake gafarta zunubai?”

50. Sai Yesu ya ce wa matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki sauka lafiya.”

Karanta cikakken babi Luk 7