Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 7:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sai tsoro ya kama su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lalle, wani annabi mai girma ya bayyana a cikinmu,” da kuma, “Allah ya kula da jama'arsa.”

17. Wannan labarin nasa kuwa ya bazu a dukan ƙasar Yahudiya da kewayenta.

18. Sai almajiran Yahaya suka gaya masa dukan abubuwan nan.

19. Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”

20. Da mutanen nan suka isa wurinsa, suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne ya aiko mu gare ka, yana tambaya, ‘Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?’ ”

21. Nan take Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani.

22. Sai ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.

23. Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”

24. Baya jakadun Yahaya sun tafi, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?

25. To, kallon me kuka je yi? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon gaske, masu zaman annashuwa, a fāda suke.

26. To, kallon me kuka je yi? Annabi? Hakika, ina gaya muku, har ya fi annabi nesa.

27. Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa,‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,Wanda zai shirya maka hanya gabaninka.’

28. Ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”

Karanta cikakken babi Luk 7