Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 4:4-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”

5. Sai Iblis ya kai shi wani wuri a bisa, ya nunnuna masa dukkan mulkokin duniya a ƙyiftawar ido.

6. Iblis ya ce masa, “Kai zan bai wa ikon duk waɗannan, da ɗaukakarsu, don ni aka danƙa wa, nakan kuma bayar ga duk wanda na ga dama.

7. In kuwa za ka yi mini sujada, duk su zama naka.”

8. Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada,Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

9. Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan,

10. don a rubuce yake cewa,‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai, su kiyaye ka,’

11. da kuma‘Za su tallafe ka,Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”

12. Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

13. Bayan da Iblis ya gama irin dukan gwaje-gwajensa, ya rabu da shi ɗan lokaci tukuna.

14. Yesu ya koma ƙasar Galili, ikon Ruhu yana tare da shi. Labarinsa ya bazu a dukan kewayen.

15. Ya yi ta koyarwa a majami'unsu, duk ana girmama shi.

16. Ya zo Nazarat inda aka rene shi. Ya shiga majami'a a ran Asabar kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe domin ya yi karatu.

17. Aka miƙa masa Littafin Annabi Ishaya, ya buɗe littafin, ya sami inda aka rubuta cewa,

18. “Ruhun Ubangiji yana tare da ni,Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara.Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru,In kuma buɗe wa makafi ido,In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,

19. In yi shelar zamanin samun karɓuwa ga Ubangiji.”

20. Ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna. Duk waɗanda suke cikin majami'a suka zuba masa ido.

21. Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.”

22. Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”

23. Yesu ya ce musu, “Lalle za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka.’ Za ku kuma ce mini, ‘Duk abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, ka yi a nan garinku mana.’ ”

Karanta cikakken babi Luk 4