Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 4:21-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.”

22. Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”

23. Yesu ya ce musu, “Lalle za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka.’ Za ku kuma ce mini, ‘Duk abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, ka yi a nan garinku mana.’ ”

24. Ya ce kuma, “Hakika, ina gaya muku, ba annabin da yake yardajje a garinsu.

25. Amma gaskiya nake gaya muku, a zamanin Iliya akwai mata gwauraye da yawa a Isra'ila, wato a lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa'ad da babbar yunwa ta game dukan ƙasar.

26. Duk da haka ba a aiki Iliya gun ko ɗaya daga cikinsu ba, sai ga wata mace kaɗai a Zarifat ta ƙasar Sidon wadda mijinta ya mutu.

27. A zamanin Annabi Elisha kuma akwai kutare da yawa a Isra'ila, ba kuwa ɗayansu da aka tsarkake sai Na'aman, mutumin Suriya, kaɗai.”

28. Da suka ji haka, duk waɗanda suke a majami'a suka husata ƙwarai.

29. Sai suka tashi suka fitar da shi bayan gari, har suka kai shi goshin dutsen da aka gina garinsu a kai, don su jefa shi ƙasa.

30. Amma ya ratsa ta tsakiyarsu, ya yi tafiyarsa.

31. Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a ƙasar Galili, yana koya musu ran Asabar.

32. Suka yi mamakin koyarwarsa domin magana tasa da hakikancewa take.

33. A majami'ar kuwa akwai wani mutum mai baƙin aljan. Sai ya ta da murya da ƙarfi ya ce,

34. “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”

35. Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Shiru! Rabu da shi!” Bayan da aljanin ya fyaɗa shi ƙasa a tsakiyarsu, ya rabu da shi, bai kuwa cuce shi ba.

36. Sai mamaki ya kama su duka, suna ce wa juna, “Wannan wace irin magana ce? Ga shi, da tabbatarwa, da gabagaɗi kuma yake umartar baƙaƙen aljannu, suna kuwa fita.”

37. Labarinsa duk ya bazu ko'ina a kewayen ƙasar.

38. Sai ya tashi daga majami'a, ya shiga gidan Bitrus. Surukar Bitrus kuwa tana fama da mugun zazzaɓi, sai suka roƙe shi saboda ita.

Karanta cikakken babi Luk 4