Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 3:5-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Za a cike kowane kwari,Kowane dutse da kowane tsauni za a baje su.Za a miƙe karkatattun wurare,Za a bi da hanyoyin da ba su biyu ba.

6. Dukkan 'yan adam kuma za su ga ceton Allah.”

7. Saboda haka, Yahaya ya ce wa taron jama'ar da yake zuwa domin ya yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?

8. Ku yi aikin da zai nuna tubanku, kada ma ku ko fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku Allah yana da iko ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan.

9. Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”

10. Sai taron suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi ke nan?”

11. Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, ya raba da marar ita, mai abinci ma haka.”

12. Masu karɓar haraji ma suka zo a yi musu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?”

13. Ya ce musu, “Kada ku karɓi fiye da abin da aka umarce ku.”

Karanta cikakken babi Luk 3