Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 3:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya,

2. a zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, Maganar Allah ta zaike wa Yahaya ɗan Zakariya a jeji.

3. Sai ya zaga duk lardin bakin Kogin Urdun, yana wa'azi, cewa mutane su tuba a yi musu baftisma, domin a gafarta musu zunubansu,

4. yadda yake a rubuce a Littafin Annabi Ishaya cewa,“Muryar mai kira a jeji tana cewa,Ku shirya wa Ubangiji tafarki,Ku miƙe hanyoyinsa,

5. Za a cike kowane kwari,Kowane dutse da kowane tsauni za a baje su.Za a miƙe karkatattun wurare,Za a bi da hanyoyin da ba su biyu ba.

6. Dukkan 'yan adam kuma za su ga ceton Allah.”

7. Saboda haka, Yahaya ya ce wa taron jama'ar da yake zuwa domin ya yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?

8. Ku yi aikin da zai nuna tubanku, kada ma ku ko fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku Allah yana da iko ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan.

Karanta cikakken babi Luk 3