Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 20:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya mini,

4. baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?”

5. Sai suka yi muhawwara da juna suka ce, “In mun ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

6. In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ sai duk jama'a su jajjefe mu, don sun tabbata Yahaya annabi ne.”

7. Sai suka amsa masa, suka ce, ba su san daga inda take ba.

8. Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”

9. Sai ya shiga ba jama'a misalin nan, ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya ba waɗansu manoma ijararta, ya kuma tafi wata ƙasa, ya daɗe.

10. Da kakar inabi ta yi, ya aiki wani bawansa a gun manoman nan su ba shi gallar garkar. Amma manoman suka yi masa dūka, suka kore shi hannu wofi.

11. Ya kuma aiki wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka wulakanta shi, suka kore shi hannu wofi.

12. Har wa yau dai ya aiki na uku, shi kuwa suka yi masa rauni, suka kore shi.

13. Sai mai garkar ya ce, ‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.’

14. Amma da manoman suka gan shi, suka yi shawara da juna suka ce, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Mu kashe shi mana, gādon ya zama namu.’

15. Sai suka jefa shi a bayan shinge, suka kashe shi. To, me ubangijin garkan nan zai yi da su?

Karanta cikakken babi Luk 20