Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 2:45-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Da ba su same shi ba, suka koma Urushalima, suna ta cigiyarsa.

46. Sai kuma a rana uku suka same shi a Haikalin zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi.

47. Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al'ajabin irin fahimtarsa da amsoshinsa.

48. Da suka gan shi suka yi mamaki, sai uwa tasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.”

49. Sai ya ce musu, “Me ya sa kuka yi ta nemana? Ashe, ba ku sani wajibi ne in yi sha'anin Ubana ba?”

50. Amma ba su fahimci maganar da ya yi musu ba.

51. Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwa tasa kuwa na riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.

52. Yesu kuwa ya yi ta ƙaruwa da hikima, da girma, da kuma tagomashi wurin Allah da mutane.

Karanta cikakken babi Luk 2