Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 18:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan marar gaskiya ya faɗa!

7. Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?

8. Ina gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa'ad da Ɗan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya ne?”

9. Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce,

10. “Waɗansu mutum biyu suka shiga Haikali yin addu'a, ɗaya Bafarisiye, ɗaya kuma mai karɓar haraji.

11. Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu'a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan.

12. Duk mako ina azumi sau biyu. Kome na samu nakan fitar da zakka.’

13. Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’

14. Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”

15. Waɗansu suka kawo masa 'yan yaransu domin ya taɓa su. Ganin haka sai almajiransa suka kwaɓe su.

16. Amma Yesu ya kira 'yan yara wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.

17. Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”

Karanta cikakken babi Luk 18