Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 11:33-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. “Ba mai kunna fitila ya ɓoye ta a rami, ko ya rufe ta da masaki. A'a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken.

34. Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka zai cika da haske. In kuwa idonka da lahani, sai jikinka ya cika da duhu.

35. Saboda haka, sai ka lura ko hasken da yake a gare ka duhu ne.

36. In kuwa duk jikinka ya cika da haske, ba inda ke da duhu, ai, duk sai ya haskaka gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila take haskaka maka.”

37. Yesu yana magana, sai wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Ya shiga cin abincin.

38. Sai Bafarisiyen ya yi mamakin ganin yadda Yesu zai ci abinci ba da fara wanke hannu ba.

39. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ku Farisiyawa kam, kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike kuke da zalunci da mugunta.

40. Ku marasa azanci! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ya yi cikin ba?

41. Gara ku tsarkake cikin, sa'an nan kome zai tsarkaka a gare ku.

42. “Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna fitar da zakkar na'ana'a da karkashi, da kuma kowane ganyen miya. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da waɗancan ba.

43. Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna son mafifitan mazaunai a majami'u, da kuma gaisuwa a kasuwa.

44. Kaitonku! Kuna kama da kaburburan da ba a gani, waɗanda mutane suke takawa da rashin sani.”

45. Sai wani a cikin masanan Attaura ya amsa masa ya ce, “Malam, faɗar haka fa, mu ma, ai, ka ci mutuncinmu.”

46. Sai Yesu ya ce, “Ku kuma kaitonku, masanan Attaura! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu!

47. Kaitonku! Don kuna gina gubbobin annabawan da kakanninku suka kashe.

48. Wato, ku shaidu ne a kan kun yarda da ayyukan kakanninku, ga shi, su ne fa suka kashe su, ku kuwa wai har kuka gina musu gubbobin!

49. Shi ya sa hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni, su kashe waɗansu,’

Karanta cikakken babi Luk 11