Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 10:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar 'yan tumaki a tsakiyar kyarketai.

4. Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko burgami, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya.

5. Duk gidan da kuka sauka, ku fara da cewa, ‘Salama alaikun mutanen gidan nan!’

6. In akwai da ɗan salama a gidan, to, salamarku za ta tabbata a gare shi. In kuwa babu, za ta komo muku.

7. Ku zauna a gidan, kuna ci kuna shan duk irin abin da suka ba ku, domin ma'aikaci ya cancanci ladansa. Kada ku riƙa sāke masauki.

8. Duk garin da kuka shiga, in an yi na'am da ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku.

9. Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’

10. Amma duk garin da kuka shiga ba a yi na'am da ku ba, sai ku zaga kwararo kwararo, kuna cewa,

11. ‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.’

12. Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.”

13. “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, sun zauna sāye da tsumma, suna hurwa da toka.

14. Amma a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.

15. Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.

Karanta cikakken babi Luk 10