Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 1:20-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. To, ga shi, za ka bebance, ba za ka iya magana ba, sai a ran da al'amuran nan suka auku, don ba ka gaskata maganata ba, za a kuwa cika ta a lokacinta.”

21. Jama'a suna ta jiran Zakariya, suna mamakin jinkirinsa a Haikali.

22. Da ya fito, ya kāsa yi musu magana. Sai suka gane lalle an yi masa wahayi ne a Haikalin. Sai ya riƙa yi musu nuni, amma ba ya magana.

23. Sa'ad da kuma kwanakin hidimarsa suka cika, ya koma gida.

24. Bayan kwanakin nan mata tasa Alisabatu ta yi ciki. Sai ta riƙa ɓuya har wata biyar, tana cewa,

25. “Haka Ubangiji ya yi mini a kwanakin da ya dube ni da rahama, domin yă kawar mini da wulakanci a wurin mutane.”

26. A wata na shida Allah ya aiko mala'ika Jibra'ilu zuwa wani gari a ƙasar Galili, wai shi Nazarat,

27. gun wata budurwa da aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu, na zuriyar Dawuda, sunan budurwar kuwa Maryamu.

28. Sai mala'ikan ya je wurinta, ya ce, “Salama alaikun, yake zaɓaɓɓiya, Ubangiji yana tare da ke!”

29. Amma ta damu ƙwarai da maganar, ta yi ta tunani ko wannan wace irin gaisuwa ce.

30. Mala'ikan kuma ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.

31. Ga shi kuma, za ki yi ciki, ki haifi ɗa, ki kuma sa masa suna Yesu.

32. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki.Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dawuda,

33. Zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada,Mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.”

34. Sai Maryamu ta ce wa mala'ikan, “Ƙaƙa wannan zai yiwu, tun da yake ba a kai ni ɗaki ba?”

Karanta cikakken babi Luk 1