Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Kol 3:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Fiye da waɗannan duka, ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala take ƙulluwa a cikinta.

15. Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.

16. Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.

17. Kome kuke yi, a game da magana ko aikatawa, ku yi duka da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.

18. Ku matan aure, ku bi mazanku yadda ya dace a cikin Ubangiji.

19. Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kada kuma ku yi musu kaushin hali.

20. Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya ta kowane hali, domin haka Ubangiji yake so.

Karanta cikakken babi Kol 3