Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 5:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Dā, ai, kuna ci gaba sosai. Wane ne ya hana ku bin gaskiya?

8. Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne.

9. Ai, ɗan yisti kaɗan, yake game dukkan curin gurasa.

10. Na dai amince da ku a cikin Ubangiji, ba za ku bi wani ra'ayi dabam da nawa ba. Wannan da yake ta da hankalinku kuwa zai sha hukunci, ko shi wane ne.

11. Amma 'yan'uwa, in da har yanzu wa'azin yin kaciya nake yi, to, don me har yanzu ake tsananta mini? In da haka ne, ashe, an kawar da hamayyar da gicciyen Almasihu yake sawa ke nan!

12. Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu babanni!

13. Ya ku 'yan'uwa, don 'yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da 'yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna.

14. Don duk Shari'a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

Karanta cikakken babi Gal 5