Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 5:14-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Don duk Shari'a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

15. Amma in kuna cin naman juna, ku mai da hankali fa, hanyar hallaka juna ke nan.

16. Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba.

17. Don halin mutuntaka gāba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gāba da halin mutuntaka. Waɗannan biyu gāba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so.

18. In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, Shari'a ba ta da iko da ku, ke nan.

19. Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci,

20. da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya,

21. da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakar da ku kamar yadda na faɗakar da ku a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.

Karanta cikakken babi Gal 5