Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 2:16-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. da yake mun sani mutum ba ya samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, sai dai ta wurin gaskatawa ga Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya ga Almasihu, ba ta wurin bin Shari'a ba, don ba ɗan adam ɗin da zai sami kuɓuta ga Allah ta hanyar bin Shari'a.

17. In kuwa ya zamana, sa'ad da muke neman kuɓuta ga Allah ta wurin Almasihu, an tarar har mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, Almasihu yana hidimar zunubi ne? A'a, ko kusa!

18. Amma in na sāke ginin abin da dā na rushe, na tabbata mai laifi ke nan.

19. Gama ni ta wurin Shari'a matacce ne ga Shari'a domin in rayu ga Allah.

20. An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.

21. Ba na tozarta alherin Allah. Don da ta wurin bin Shari'a ake samun adalcin Allah, ashe, da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”

Karanta cikakken babi Gal 2