Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Filib 3:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Muradina ke nan, in san Almasihu, in san ikon tashinsa daga matattu, in yi tarayya da shi a shan wuyarsa, in kuma zama kamarsa a wajen mutuwarsa,

11. domin ta ko ƙaƙa in kai ga tashin nan daga matattu.

12. Ba cewa, na riga na kai ga waɗannan ba ne, ko kuwa na zama kammalalle, a'a. sai dai ina nacewa ne, in riƙi abin nan da Almasihu Yesu ma ya riƙe ni saboda shi.

13. Ya 'yan'uwa, ban ɗauka a kan cewa na riga na riƙi abin ba, amma abu guda kam ina yi, ina mantawa da abin da yake baya, ina kutsawa zuwa ga abin da yake gaba.

14. Ina nacewa gaba gaba zuwa manufar nan, domin in sami ladar kiran nan zuwa sama, da Allah ya yi mini ta wurin Almasihu Yesu.

15. Saboda haka ɗaukacin waɗanda suka kammala a cikinmu, sai su bi wannan ra'ayi. In kuwa a game da wani abu ra'ayinku ya sha bambam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma.

16. Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.

17. Ya ku 'yan'uwa, ku yi koyi da ni dukanku baki ɗaya, ku kuma dubi waɗanda zamansu yake daidai da gurbin da muka bar muku.

18. Domin da yawa waɗanda na sha gaya muku, yanzu kuma nake gaya muku, har da hawaye, suna bin Yesu, in ji su, amma su magabtan gicciyen Almasihu ne.

19. Ƙarshensu hallaka ne, Allahnsu ciki ne, rashin kunyarsu ita ce abar taƙamarsu, sun ƙwallafa ransu a kan al'amuran duniya.

20. Mu kuwa 'yan Mulkin Sama ne, daga can ne kuma muke ɗokin zuwan Mai Ceto, Ubangiji Yesu Almasihu,

21. wanda zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, ya mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka, da ikon nan nasa na sarayar da dukkan abubuwa a gare shi.

Karanta cikakken babi Filib 3