Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Filib 3:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A ƙarshe kuma 'yan'uwa, ku yi farin ciki da Ubangiji. Sāke rubuto muku waɗannan abubuwa bai gundure ni ba, ga shi kuwa, domin lafiyarku ne.

2. Ku yi hankali da karnukan nan! Ku yi hankali da mugayen ma'aikatan nan! Ku yi hankali da masu yankan jikin nan!

3. Don mu ne masu kaciyar ainihi, masu bauta wa Allah ta wurin Ruhu, masu taƙama da Almasihu Yesu, ba mu kuma dogara da al'amuran ganin ido,

4. ko da yake ni ina iya dogara da al'amuran ganin ido, in dai nake so. In kuma akwai wanda yake tsammani yana iya dogara ga al'amuran ganin ido, to, ni na fi shi.

5. An yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra'ila ne, na kabilar Biliyaminu, Ba'ibrane ɗan Ibraniyawa, bisa ga Shari'a kuwa ni Bafarisiye ne,

6. a wajen himma kuwa mai tsananta wa Ikkilisiya ne ni, wajen aikin adalci kuwa bisa ga tafarkin Shari'a, marar abin zargi nake.

7. Amma dai kowace irin riba na taɓa ci, na ɗauka hasara ce saboda Almasihu.

8. Dahir na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar sanin da nake yi na Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tozari domin Almasihu yă zama nawa,

9. a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina ba, wanda ya danganta da bin Shari'a, sai dai da adalcin nan wanda yake tsirowa daga bangaskiya ga Almasihu, wato, da adalcin nan wanda yake samuwa daga Allah ta wurin bangaskiya.

10. Muradina ke nan, in san Almasihu, in san ikon tashinsa daga matattu, in yi tarayya da shi a shan wuyarsa, in kuma zama kamarsa a wajen mutuwarsa,

11. domin ta ko ƙaƙa in kai ga tashin nan daga matattu.

12. Ba cewa, na riga na kai ga waɗannan ba ne, ko kuwa na zama kammalalle, a'a. sai dai ina nacewa ne, in riƙi abin nan da Almasihu Yesu ma ya riƙe ni saboda shi.

13. Ya 'yan'uwa, ban ɗauka a kan cewa na riga na riƙi abin ba, amma abu guda kam ina yi, ina mantawa da abin da yake baya, ina kutsawa zuwa ga abin da yake gaba.

14. Ina nacewa gaba gaba zuwa manufar nan, domin in sami ladar kiran nan zuwa sama, da Allah ya yi mini ta wurin Almasihu Yesu.

Karanta cikakken babi Filib 3