Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Filib 2:13-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Domin Allah shi ne mai aiki a zukatanku, ku nufi abin da yake kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.

14. Kome za ku yi, kada ku yi da gunaguni, ko gardama,

15. don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,

16. kuna riƙe da maganar rai kankan, har a ranar bayyanar Almasihu in yi taƙama, cewa himmata da famana ba a banza suke ba.

17. Ko da za a tsiyaye jinina a kan hadaya da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farin ciki, in kuma taya ku farin ciki, ku duka.

18. Haka ku ma, ya kamata ku yi farin ciki, ku kuma taya ni farin ciki.

19. Ina sa zuciya ga Ubangiji Yesu in aika muku da Timoti da wuri, don ni ma in ƙarfafa da samun labarinku.

20. Ba ni da wani kamarsa, wanda da sahihanci zai tsananta kula da zamanku lafiya.

21. Dukansu sha'anin gabansu kawai suke yi, ba na Yesu Almasihu ba.

22. Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.

23. Shi ne nake fata in aiko, da zarar na ga yadda al'amarina yake gudana.

24. Na kuma amince har ga Ubangiji, ni ma da kaina ina zuwa ba da daɗewa ba.

25. Amma na ga lalle ne in aiko muku da Abafaroditas ɗan'uwana, abokin aikina, abokin famana kuma, wanda kuka aiko ya yi mini ɗawainiya.

Karanta cikakken babi Filib 2