Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Filib 1:2-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu, su tabbata a gare ku.

3. Ina gode Allahna duk sa'ad da nake tunawa da ku,

4. a kullum kuwa a kowace addu'a da nake muku duka, da farin ciki nake yi.

5. Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu.

6. Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu.

7. Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.

8. Domin Allah shi ne mashaidina a kan yadda nake begenku duka, da irin ƙaunar da Almasihu Yesu yake yi.

9. Addu'ata ita ce, ƙaunarku ta riƙa haɓaka da sani da matuƙar ganewa,

10. domin ku zaɓi abubuwa mafifita, ku zama sahihai, marasa abin zargi, har ya zuwa ranar Almasihu,

11. kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.

12. 'Yan'uwa, ina so ku sani, al'amuran nan da suka auku a gare ni, har ma sun yi amfani wajen yaɗa bishara,

13. har dai ya zama sananne ga dukan sojan fāda da sauran jama'a, cewa ɗaurina saboda Almasihu ne.

14. Har ma galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka ƙarfafa saboda ɗaurina, sun kuma ƙara fitowa gabagaɗi, su faɗi Maganar Allah ba tare da tsoro ba.

15. Lalle waɗansu suna wa'azin Almasihu saboda hassada da husuma, amma waɗansu kam, saboda kyakkyawar niyya ne.

16. Waɗannan suna yi ne a kan ƙauna, sun sani, an sa ni nan ne domin kāriyar bishara.

Karanta cikakken babi Filib 1